<?xml version="1.0" encoding="UTF-8"?><song><title>In Za Ka Bi Mai Cetonmu LW143</title>
<lyrics>[V1]
 1) In za ka bi Mai Cetonmu,
 Lura da wannan tun yanzu,
 Ba za ya karƃi kome ba,
 In ba ka ba shi ranka ba.

[V2]
 2) Aikinka kawai ba ya so,
 Ba ya bukatar taimako.
 In ba ka ƙaunace shi ba,
 Aikinka ba zai karƃa ba.

[V3]
 3) Kayanka kuma ba ya so,
 Ba domin kaya ba ya zo.
 In ba ka ba shi ranka ba,
 Kayanka ba zai karƃa ba.

[V4]
 4) Gama ya bar gidansa can,
 Ya ba da jininsa a nan,
 Garin ya sayi zuciyarka.
 Bar shi ya karƃi mulkinta.</lyrics>
<hymn_number>143</hymn_number>
<author>Hatton, John (1710-1793), Watts, Isaac (1674-1748)</author>
</song>